{"id":12376,"date":"2018-10-04T18:57:48","date_gmt":"2018-10-04T18:57:48","guid":{"rendered":"https:\/\/everyday.ng\/?p=12376"},"modified":"2018-10-04T18:57:48","modified_gmt":"2018-10-04T18:57:48","slug":"hausa-abin-nazari-ga-kiristoci-kadai-a-rashin-sani-kaza-ta-kwanna-a-kan-dami-da-yunwa-3","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/everyday.ng\/?p=12376","title":{"rendered":"Hausa: Abin nazari ga Kiristoci kadai: A Rashin sani kaza ta kwanna a kan dami da yunwa 3"},"content":{"rendered":"<p><strong>Me ka Sani game da kalmomin Isah Almasihu?\u00a0<\/strong><br \/>\nDaga <strong>Saminu Kadaura<\/strong>, Asaba.<br \/>\nA wata karo shugabanni da ke gaba da ayukan Isah Almasihu suka aiki dogarai su<br \/>\nkama shi. Da dogaran suka saurari koyaswarsa sai suka koma ba su kama shi ba. Shugabannin suka tambayi su, \u201cDon me ba ku kawo shi ba\u201d? Sai suka bada amsa cewa: \u201cBa mutumin da ya taba Magana kamar wannan,\u201d Yah.8:2<br \/>\nMasu ilimin kimiyya sun ce, daga hasken rana ne wata da taurari ke samun<br \/>\nhaskensu. To in dai rana na haskakawa, wa ke bukatan na wata? Sauran addinai da<br \/>\nmutane suka kago kamar hasken wata da na taurari ne. Babu anfani in da akwai<br \/>\nhasken rana. Ba a ma ganin haskensu.<br \/>\nIsa Almasihu ya ce: \u201cNine hasken duniya.\u201d Hasken rana ba ta raguwa, haka nan ne<br \/>\nhasken Almasihu ga dukan mutane. A kullum yana haskakawa sai dai in wani abuya tsaya tsakanin mutane da haskensa kamar zunubi da rashin gaskatawa shine zaihana haskensa haskakawa zuciyar mutane. In mun kawar da makantar da ke hana haskensa shiga zuciyarmu, zai haskaka mu, ya yantar da mu daga zama cikin duhu. Haske ne maganin duhu.<br \/>\nIsah Almasihu ya ce: \u201cNi ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa<br \/>\nwurin Uba sai ta wurina\u201d Duk sauran annabawa sun zo su nuna hanya zuwa wurin Allah. Suna cewa wannan ita ce hanya zuwa wurin Allah. Wannan ita ce hanyarAllah. Ka aikata wanan abu. Ka bi wannan koyaswa. Ka bi umurnin wannan<br \/>\ndokoki. Amma annabi Isah Almasihu ya ce: \u201cNine hanyar, ka bi ni\u201d<br \/>\nBari mu yi misali kamar haka\u037e ka yi bakunci zuwa wata gari da amininka ya<br \/>\ngayyace ka. Da ka iso garin, ba ka kuma san gidan amininka ba, sai ka je oficin<br \/>\nma\u2019aikatan tsaro kana tambayarsu. Daya daga cikinsu ya taso yana maka kwatance,<br \/>\nka kuma rasa gane kwatancensa, nan sai ga wani dattijo ya zo ya riko hanunka ya<br \/>\nce ai ni cikin gidan nake, zo ka bi ni, zan kai ka gidan. Nan da nan na san za ka yi<br \/>\nfarin ciki ka baro ma\u2019aikacin tsaron ka biyo dattijon ya kai ka gidan amininka.<br \/>\nWannan ma\u2019aikacin tsaron yana kwatanci nuna maka hanya zuwa gidan amininka<br \/>\namma dattijon shine hanyar zuwa gidan amininka. Yesu Almasihu ya ce: \u201cNine<br \/>\nhanyar \u2013 hanya zuwa mulkin Allah. A karshe ya ce: \u201cKu zo gare ni dukanku masu<br \/>\nwahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku\u201d Mat.11:28. Hausawa na<br \/>\ncewa a san mutum da kalmarsa.<br \/>\n\u25aa<strong>Don karin bayani ko tambaya ka tuntubi Saminu Kadaura (08034152198).\u00a0Malam Kadaura yana zama cikin Asaba a jihar Delta<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Me ka Sani game da kalmomin Isah Almasihu?\u00a0 Daga Saminu Kadaura, Asaba. A wata karo shugabanni da ke gaba da ayukan Isah Almasihu suka aiki dogarai su kama shi. Da dogaran suka saurari koyaswarsa sai suka koma ba su kama shi ba. Shugabannin suka tambayi su, \u201cDon me ba ku kawo shi ba\u201d? Sai suka [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":7,"featured_media":12107,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[5772],"tags":[],"class_list":["post-12376","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","category-faith"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/everyday.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/12376","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/everyday.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/everyday.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/everyday.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/7"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/everyday.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=12376"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/everyday.ng\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/12376\/revisions"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/everyday.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=12376"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/everyday.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=12376"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/everyday.ng\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=12376"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}