Me ka Sani game da kalmomin Isah Almasihu?
Daga Saminu Kadaura, Asaba.
A wata karo shugabanni da ke gaba da ayukan Isah Almasihu suka aiki dogarai su
kama shi. Da dogaran suka saurari koyaswarsa sai suka koma ba su kama shi ba. Shugabannin suka tambayi su, “Don me ba ku kawo shi ba”? Sai suka bada amsa cewa: “Ba mutumin da ya taba Magana kamar wannan,” Yah.8:2
Masu ilimin kimiyya sun ce, daga hasken rana ne wata da taurari ke samun
haskensu. To in dai rana na haskakawa, wa ke bukatan na wata? Sauran addinai da
mutane suka kago kamar hasken wata da na taurari ne. Babu anfani in da akwai
hasken rana. Ba a ma ganin haskensu.
Isa Almasihu ya ce: “Nine hasken duniya.” Hasken rana ba ta raguwa, haka nan ne
hasken Almasihu ga dukan mutane. A kullum yana haskakawa sai dai in wani abuya tsaya tsakanin mutane da haskensa kamar zunubi da rashin gaskatawa shine zaihana haskensa haskakawa zuciyar mutane. In mun kawar da makantar da ke hana haskensa shiga zuciyarmu, zai haskaka mu, ya yantar da mu daga zama cikin duhu. Haske ne maganin duhu.
Isah Almasihu ya ce: “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa
wurin Uba sai ta wurina” Duk sauran annabawa sun zo su nuna hanya zuwa wurin Allah. Suna cewa wannan ita ce hanya zuwa wurin Allah. Wannan ita ce hanyarAllah. Ka aikata wanan abu. Ka bi wannan koyaswa. Ka bi umurnin wannan
dokoki. Amma annabi Isah Almasihu ya ce: “Nine hanyar, ka bi ni”
Bari mu yi misali kamar haka; ka yi bakunci zuwa wata gari da amininka ya
gayyace ka. Da ka iso garin, ba ka kuma san gidan amininka ba, sai ka je oficin
ma’aikatan tsaro kana tambayarsu. Daya daga cikinsu ya taso yana maka kwatance,
ka kuma rasa gane kwatancensa, nan sai ga wani dattijo ya zo ya riko hanunka ya
ce ai ni cikin gidan nake, zo ka bi ni, zan kai ka gidan. Nan da nan na san za ka yi
farin ciki ka baro ma’aikacin tsaron ka biyo dattijon ya kai ka gidan amininka.
Wannan ma’aikacin tsaron yana kwatanci nuna maka hanya zuwa gidan amininka
amma dattijon shine hanyar zuwa gidan amininka. Yesu Almasihu ya ce: “Nine
hanyar – hanya zuwa mulkin Allah. A karshe ya ce: “Ku zo gare ni dukanku masu
wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku” Mat.11:28. Hausawa na
cewa a san mutum da kalmarsa.
▪Don karin bayani ko tambaya ka tuntubi Saminu Kadaura (08034152198). Malam Kadaura yana zama cikin Asaba a jihar Delta