22.6 C
Lagos
Sunday, December 29, 2024

Hausa: Abin nazari ga Kiristoci kadai: A rashin sani kaza ta kwan a kan dami da yunwa 2

Must read

ME KA SANI GAME DA HALIN ISA ALMASIHU
Daga Saminu Kadaura.
Ya kasance cikakke. Bai taba yin zunubi ba. Bai taba yin kuskuri ba. Bai taba rokon gafarar zunubansa ba. Duk mai tsoron Allah dole ne ya furta zunubansa ya kuma roki gafara. Annabi Dauda ya roki gafarar zunubansa, Ibrahim ya yi. Zahiri akwai wani annabin da ya ce shi yana rokon gafarar zunubansa gun Allah sau saba’in a kowace rana. Za ka iya yin bincike cikin Littafi Mai Tsarki da Kur’ani amma ba za ka sami inda aka ce Yesu Almasihu ya roki gafarar zunubansa ba. Ba ya bukatan a gafarta masa domin ba shi da zunubi. Aminansa sun rubuto game da shi cewa; “Bai san zunubi ba, Bai yi zunubi ba. Babu zunubi ko aibu a gare shi.” Mutane ne da suka san shi sosai. Allah ya gafarta wa annabawan da suka furta zunubansu, amma Yesu Almasihu ba ya bukatar gafartawa. Ba shi da zunubi. Ya ma ce wa abokan gabar sa: “A cikinku wa zai iya hakkakewa na taba yin zunubi?” (Yah.8:46). Ba ko dayansu da ya nuna zunubi ko da guda daya ne ma a rayuwarsa. Wanene a cikinmu da zai buga kirji ya kalubalance abokan gabansa haka nan? An kawo Yesu a gaban alkali Bilatus, aka kuma yi masa shaidar zur, amma Bilatus bai iya samun wani laifi ba, sai ya wanke hanunsa, ya ce; “Ba ni da laifi daga jinin wannan mutumin.” Babu dan Adam a duniyan nan wadda ba shi da zunubi. Annabi Isa Almasihu shi kadai ne ya yi rayuwa a duniya mara zunubi. Ya kasance shi na musamman ne, ba shi kuma misultuwa.
Ya nuna kauna da jinkai ga duk attajirai da matalauta. Ya taba kuturu ya warkar da shi, ya ziyarci attajiri mai karban haraji don ya kubutar da shi daga mummunan halin cuta da yake yi. Isa Almasihu yana da halin yafiya, ya roki Allah ya yafe wa mutanen da suka giciye shi don ya mutu, ya ce; “Ya Uba ka yi masu gafara don ba su san abinda suke yi ba,” (Luk.23:34).
Ya umurci almajiransa su kaunaci magabtansu, su yi addu’a ma wadanda suke tsananta masu. Ya ce su rama mugunta da nagarta. Wani annabi ne ya kasance da irin wannan hali a duniya in ba annabi Isa Almasihu ba.
Don karin bayani ko tambaya ka tuntubi Saminu Kadaura (08034152198). Malam Kadaura yana zama cikin Asaba a jihar Delta

- Advertisement -spot_img

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Related articles